C2.1 Hanyoyin Sadarwa

Ɗalibai sub a da bayanin hanyoyin sadarwa na gargajiya da na zamani, da kuma sabuwar fasahar sadarwa. A yi amfani da talabijin da rediyo da bidiyo da kwamfuta da intanet da talagiram da wayar salula da hotuna wajen koyar da ɗalibai. Daga ƙarshen darasi, ɗalibai su amsa tambayoyi.

Ma'anar Sadarwa

Hanyar Sadarwa tsararriyar hanya ce da ake tsarawa ta aika saƙo ko bayani daga wuri zuwa wani wuri mai nisa. A kasar Hausa a zamunna da suka shude, ana amfani ne da kafafen sadarwa ne wajen yada bayanai, sanarwa da isar da sakon hukuma ko masarauta ga talakawansu.

Ire-iren hanyoyin sadarwa

  1. Na gargajiya
  2. Na zamani
  3. Na sabuwar fasahar sadarwa

Hanyoyin Sadarwa Na Gargajiya

Bahaushe yana amfani da kayan kiɗa na gargajiya wajen isar da saƙonni, wasu lokuttan kuwa yak an yi amfani da sanarwar baki ko yin yekuwa. Daga ciki akwai:

  1. Kiɗa
  2. Ƙuge
  3. Kwarya
  4. Tambari
  5. Ganga
  6. Ƙaho
  7. Makamashi
  8. Bindiga
  9. Wuta
  10. Hayaki
  11. Ihun yekuwa na baka wato shela

Hanyoyin Sadarwa Na Zamani

Bayan zuwan turawa, an ƙara bunƙasa hanyoyin sadarwa inda aka kawo hanyoyi na zamani, ga wasu daga cikin misalan hanyoyin sadarwa na zamani:

  1. Gidan waya
  2. Wasiƙa
  3. Wasiƙar kan sarki
  4. Wasiƙar talagiram
  5. Wasiƙar ƙarbi da kanka
  6. Kar-ta-kwana
  7. Gidan buga waya
  8. Wayar tarho
  9. Wayar talas wato tangaraho oba-oba

Sabuwar Fasahar Sadarwa

Bayan wani zamani an ƙara bunƙasa hanyoyin sadarwa a faɗin duniya, inda aka kawo hanyoyin sadarwa na zamani irinsu intane da wayar salula, waɗannan hanyoyin sadarwa sun samu karbuwa a faɗin duniya baki ɗaya.

Ga misalan wasu daga cikin sabuwar fasahar sadarwa:

  1. Rediyo
  2. Talabijin
  3. Satilayit
  4. Kwamfuta
  5. Fas
  6. Intanet
  7. Wayar hannu wato salula

Aikin Aji

  1. Ba da bayanan ire-iren hanyoyin sadarwa guda biyar da ku ka sani.
(c) Ilimin Hausa | Bello Hamisu Ida

Post a Comment

0 Comments