Siyasar Najeriya: Rahotanni Kan Tattaunawar Kawance Tsakanin Jonathan da Peter Obi Domin 2027


Siyasar Najeriya: Rahotanni Kan Tattaunawar Kawance Tsakanin Jonathan da Peter Obi Domin 2027


Yayin da zaɓen shugaban ƙasa na 2027 ke kara gabatowa, ‘yan siyasa a Najeriya na ƙara hura wutar shirye-shiryen su da dabarun da za su iya kai su ga nasara. A yanzu haka, ana samun labarai da dama kan yiwuwar ƙulla kawance tsakanin manyan ‘yan siyasa don fuskantar gwamnatin APC mai ci.

Rahotanni daga farkon mako sun nuna cewa akwai tattaunawa tsakanin bangaren tsohon shugaban ƙasa, Goodluck Jonathan, da na Peter Obi — ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Labour Party (LP) a zaɓen 2023. Wannan yunkuri na iya zama wani mataki na haɗa ƙarfi da ƙarfe domin fuskantar babban zaɓe mai zuwa.

A ƙarshen makon da ya gabata, tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC, Dumebi Kachikwu, ya bayyana a taron manema labarai a Abuja cewa Jonathan ya yi wa Peter Obi tayin zama Ministan Kuɗi da Tattalin Arziki idan zai jingine takarar sa a 2027. Sai dai jam’iyyar PDP, wadda Jonathan ya fito, ta ce ba ta da masaniya kan wannan magana, amma za ta yi maraba da Obi idan ya koma cikinta.

Kakakin jam’iyyar PDP na ƙasa, Ibrahim Abdullahi, ya shaida wa BBC cewa:

“Ai dama Peter Obi namu ne, kawai matsala ce ta sa ya fita a kakar zaɓen da ta gabata. Idan ya dawo yanzu, ba abin mamaki ba ne.”


Ibrahim ya ce jam’iyyar PDP za ta yi maraba da kowace irin haɗaka idan manufarta ta kasance samar da maslaha ga ƙasa.

A gefe guda kuma, wani kusa da Peter Obi, Ibrahim Hussain Abdulkarim, ya ce masu ƙulla irin waɗannan maganganu na da wata manufa ce ta 2031. Ya ce duk da kyakkyawar alaƙar Obi da Jonathan tun lokacin gwamnatin sa, Obi ba zai yarda ya karɓi muƙamin minista ba a wannan lokaci.

“A yanzu ba magana ce ta dawowa ba, magana ce ta yin gaba. Mun riga mun yi aiki a gwamnatin Jonathan, yanzu gaba muke kallo,” in ji shi.


Ya ƙara da cewa idan za a yi haɗaka, to zai fi dacewa Jonathan ya mara wa Obi baya domin a samu sauyi a ƙasar.

Sai dai PDP ta bayyana cewa a shirye take ta bai wa kowa dama ya tsaya takara a fitar da ɗan takarar ta, kuma duk wanda ya yi nasara a zaɓen fidda gwani, jam’iyyar za ta goya masa baya.

Masanin harkokin siyasa, Farfesa Abubakar Kari, ya yi tsokaci kan yiwuwar haɗin gwiwar Jonathan da Obi, inda ya ce hakan na iya amfani ga dukkansu, musamman saboda duka biyu suna da ƙarfi a yankunan kudu maso gabas da kudu maso kudu. Amma ya yi gargadi cewa idan suka tsaya takara tare, za su iya raba kuri’un yankunansu, wanda zai rage musu dama.

“A siyasa babu abin da ba zai yiwu ba, ko da yake akwai masu iya zuga Obi kada ya amince. Amma idan aka ba shi muƙamin Ministan Tattalin Arziki, zai dace da shi, domin yawancin maganganunsa kan tattalin arziki ne,” in ji Farfesa Kari.


Duk da haka, masana na ganin akwai sauran lokaci kafin a iya hasashen abin da zai faru, musamman ganin yadda yanayin siyasar ƙasar ke ci gaba da sauyawa. Duk da bambance-bambancen ra’ayi, abu guda da masu hamayya da APC suka haɗu a kai shi ne bukatar samun haɗin kan ‘yan adawa don tunkarar gwamnatin Bola Tinubu a 2027.



Post a Comment

0 Comments