Ana wadannan bukukuwan ne bayan kammala azumin watan Ramadan da kuma ƙarshen shekarar musulumci. Shi hawan salla biki ne da sarakuna ke gabatarwa a ranakun ƙaramar sallah da babbar sallah, akan fara bikin hawan sallah ne daga filin idi. Sarki yana yin ƙasa da kyalliya ya hau dokinsa tare da hakimansa da digantansa da sauran masu riƙe da muƙaman sarautar gargajiya.
Kowane ɗaya daga cikinsu zai hau dawakai da tawagarsa cikin kwalliya daga su har dawakan nasu, suna tafiya jama'a kuma na kewaye da su suna kallo suna miƙa gaisuwa. A ranar farko a kan tashi daga filin idi zuwa gidan sarki. Idan aka je gidan sarki, sai a jira sarki ya zo ya sauka tukuna, sannan duk sauran hakimansa ɗaya-bayan-ɗaya su je su yi gaisuwa. Bayan an kammala kuma sai sarki ya yi jawabi ga jama'ar ƙasarsa baki ɗaya sannan a sallami kowa ya watse.
Washegari kuma sai a ci gaba, wanda wannan ya kan bambanta daga masarauta zuwa wata masarautar. Kowace masarauta akwai takamaiman wani guri da sarki ke zuwa a wannan rana, su kuma jama'a su fito gefen hanya suna miƙa gaisuwa ga sarki, fadawa kuma suna karɓa.
Bayanin Bikin Maulidi
Maulidi wani biki ne da Musulmai ke yi duk shekara don tunawa da haihuwar Manzo Allah Annabi Muhammad (saw). Ana yin Maulidi ne a duk 12 ga watan Rabi' al-awwal ta shekarar Hijira. Musulmi a fadin duniya ne ke bikin maulidin kuma suna fitowa domin bayyana farin cikinsu.
Ana karatun Al'kur'ani da kuma jawabai na tarihi da fadakarwa ne a guraren taron maulidi; hade da shagulgulan walima da wakokin yabo ga Manzon Allah (s.a.w) don bayyana farin ciki.
Muhimmancin Bukukuwan Sallah
- Ana gabatar da ibada mai muhimmanci watau sallah idi a ranar sallah.
- Bukukuwan Sallah na ƙara danƙon zumunci, inda ake kai ziyara gidajen yan'uwa da abokan arziƙi.
- Bukukuwan sallah ya saka annashuwa da nishaɗi inda ake ciye-ciye da lashe-lashe don nuna murna.
- Ana raya al'adu a ranar bukukuwan sallah, inda ake yin hawan sallah na ƙawa.
Aikin Aji
- Ba da bayanin ire-iren bukukuwan salla?
- Kawo muhimmancin yin bukukuwan guda biyar?
0 Comments