Ɗalibai su karanta rubutattun waƙoƙin Hausa, su rera rubututtun waƙoƙi tare da bayyana manufar waƙa. A yi amfani da litattafai da rediyo da talabijin da bidiyo da kaset da rikoda wajen koyar da ɗalibai. Daga ƙarshen darasi ɗalibai su amsa tambayoyi.
Ma'anar Waƙa Rubutacciya
Ana iya siffanta waƙa da aunanniyar magana. Ita kuwa rubutacciyar waƙa, rubutata ake yi, wasu rubutattun waƙoƙi ana rera su daga baya. Haka kuma rubutacciyar waƙa tana da ma'auni da sai ta hau kansa kafin ta zama cikakkiyar waƙa.
Rubutacciyar wakar Hausa ta samu tasiri ne daga wakokin Larabci, domin kuwa ba a san ta ba sai da Musulunci da ilimin Larabci su ka shigo kasar Nijeriya, wato musamman lokacin jihadin Shehu Usmanu.
Karanta Rubutacciyar Waƙa Daga Littafi
Misalin rubutacciyar waƙa ta Mu'azu Haɗeja mai taken: 'Gaskiya bata sake gashi'.
Kuma sai kabi wanda ya haife ka
Ka kiyaye hududulLahi suna
nan amru da nahyu suna kanka
Wallahi Uwa da Uba sune
Hanyarka ta neman albarka
In sun gajiya bisa zamani
Sai ka dau wahalarsu da karfinka
Yi fata kadda ka sabe su
Wata rana Allah zai saka
Abinda ka shuka don ka sani
Shine ka tsirowa gonarka
In hairi, hairi zaka gani
In sharri, sharri zai bi ka
Wa adi'ulLahu fadar Allah
Kuma girmama wanda ya girme ka
Duk wanda ya raina fadar Allah
Shi ya bata ya auka halaka
Duk wanda ya raina fadar Allah
Shine muka cewa Dan Iska
Har shina wa kansa kirari, sau
rara kaji taken dan iska
Dan iska sandan Kuka da sun
gumi nai ba;a yin taki
Dusar buntu ba'a ba dabba
To kaji kirarin dan iska
Dan iska naman Balbela
Ba a cin shi da na Hankaka
Kilishin Jaba sai dan iska
Ba mai ci sai ko mai shirka
Kashin Bera baya taki
Balle kayi dokin ga-na-ka
Kiwon Yimka, kiwon banza
Wata ran zai gallabi yayanka
Bayanin Yadda Ake Karanta Waƙa
Wajen karanta rubutacciyar waƙa, a lura da wasu abubuwa kamar baitin waƙa, amsa-amon waƙa da kuma ƙafiya. Ga bayaninsu kamar haka:
- Ana rubuta waƙa ne a layi-layi wanda ake kiran kowane layi guda ɗango.
- Waɗannan layuka (ɗangwaye) guda biyu zuwa biyar su suke samar abin da ake kira baiti.
- Ƙarshen kowane ɗango (layi) na kowane baiti akan so ya ƙare da sauti iri ɗaya, wannan shi ake kira amsa amo ko kuma ƙafiya.
Bayanin Wasu Keɓaɓɓun Kalmomi Na Waƙa
| Uwa | Mahaifiya. |
| Uba | Mahaifi. |
| Hanyarka | Hanyar da mutum ya zaɓi bi a cikin rayuwarsa. |
| Albarka | Abun da ke da daraja a cikin rayuwa. |
| Gajiya | Ƙosawa da yin wani abu. |
| Zamani | Lokacin da wani abu ke faruwa a cikin zamani. |
| Shuka | Ayyukan da ake aikatawa masu kyau ko maras sa kyau. |
| Tsirowa | Fitowa daga cikin ƙasa. |
| Gonarka | Inda ake noma hatsi, amma a nan an misalta gona da inda ake tara ayyukan alƙairi da aka aikata. |
| Hairi | Ayyukan alƙairi da aka aikata. |
| Sharri | Ayyukan sharri da aka aikata. |
| Wa adi'ulLahu | Da bin Allah Maɗaukakin Sarki. |
| Girmama | Nuna girma da wanda ya fi ku shekaru. |
| Auka | Wanda ya faɗa cikin ɓata. |
| halaka | Halaka na nufin ɓata wato ruɗin duniya. |
| Ɗan Iska | Wanda baya da kirki, marar jin maganar iyayensa da sauran al'umma. |
| Gumi | Zufar da ke fita in ana aikin ƙarfi. |
| Taki | Taki da ake zuba wa a gona. |
| Naman balbela | Naman jikin balbela wanda baƙi ne. |
| Hankaka | Nau'in tsuntsu ne. |
Manufar Waƙar
Manufar waƙar gaskiya bata sake gashi wadda Mu'azu Haɗeja ya rubuta, an rubutata ne domin a nuna gaskiya sannan a yi nuni da hanyoyin da ake aikata ayyukan alkairi, a ɗayan ɓangaren kuma a nuna ƙarya sannan a yi nuni da makomar maƙaryaci.
Aikin Aji
- Karanta rubutattun waƙoƙi.
- Sake rera rubutacciyar waƙa da aka karanta a cikin aji.
- Bayyana manufar waƙar?
0 Comments