Ɗalibai su karanta was an kwaikwayo su bayyana yadda kowane ɗan wasa yake fitowa a cikin wasa. A yi amfani da litattafai da rediyo da talabijin da bidiyo da sidi. Daga ƙarshen darasi, ɗalibai su amsa tambayoyi.
Karanta Littafin Wasan Kwaikwayo
Wasan kwaikwayo, kamar yadda sunan ya nuna, wasa ne da ake gina shi kan wani labari, ko wata matsala ta rayuwa da ake son nusarwa ga jama'a don ilmantar da su daga hanyar da ta dace da rayuwa, cikin siffar yakini wato zahiri.
Wasan kwaikwayo a Ƙasar Hausa yana da nau'o'in sanannu guda biyu, ya rabu zuwa nau'o'I kamar haka:
- Wasannin kwaikwayo na Gargajiya
- Wasannin kwaikwayo na Zamani
Wasannin Kwaikwayo Na Gargajiya
Wasannin kwaikwayo na gargajiya wasanni ne da Bahaushiyar al'ada ta yarda da su, waɗanda daga cikin wasannin akan yi su, ko a gabatar da su a kowane lokaci. Wasu kuma daga cikinsu akwai lokutan da ba a yin su, wasu kuma akan gabatar da su shekara-shekara kuma akan yi su a wasu lokutan bukukuwan al'ada. Misali a lokacin watan Azumi akan yi wasan tashe da kuma lokutan kaka inda akan yi wasan buɗar dawa da cin tumu da sauransu.
Wasannin Kwaikwayo Na Zamani
Rubutaccen wasan kwaikwayo, da yake a rubuce ake samar da shi, an san lokacin da aka fara yin sa. Shi rubutaccen wasan kwaikwayo kuwa mai gajeren tarihi ne, in an kwatanta shi da sauran ɓangarori na adabin zamani na Hausa.
Wasan Buɗar Dawa
Wasan Buɗar dawa wasan kwaikwayo ne da Hausawa ke yi shekara-shekara don neman tsari daga cututtukan shekara da kuma sanin abinda shekarar za ta kawo. Bokaye da Maharba da Manoma su suke shugabantar wannan buki. Anayin wannan biki ne bayan ruwan damina ya ɗauke da wata huɗu. Idan wannan wata na huɗu ya kama ranar sha huɗu ake gudanar da wannan wasa.
Yadda Ake Yin Wasan Buɗar Dawa
Yanda ake aiwatar da shi wannan wasa na Buɗar dawa shi ne dazarar damina ta wuce, bayan wata huɗu ake yin wannan wasa, tun kafin lokacin za'a sanar da mutanen gari da na ƙauyuka, wato dai ana karaɗe gari ne da shela tare faɗin ranar da za ayi. Haka zalika za a fitar da ƙauyen da za a gudanar da wasan tare da dajin da za a je.
Yadda Kowane Ɗan Wasa Ke Fitowa
Mutanen da ke aiwatar da wasan Buɗar dawa su ne kamar haka:
- Manoma
- Mafarauta
- Bokaye
- Mutanen gari
Aikin Aji
- Karanta wasan kwaikwayo na uwar gulma.
- Ba da bayanin yadda kowane ɗan wasa yake fitowa a wasa.
- A shirya wasan kwaikwayo a cikin aji, a lura da yadda ake fitar da yan wasa.
© Ilimin Hausa | Bello Hamisu Ida
0 Comments