📖 A2.1 Karatu Don Auna Fahimta – Hausa Language Lesson (Primary 6)
Wannan darasi yana koyar da É—alibai karatu don auna fahimta. Za su karanta labari, fitar da muhimman kalmomi da ma’anarsu, sannan su amsa tambayoyi.
🎯 Manufar Darasi
- ÆŠalibai su karanta labari da kansu.
- Su bayar da labarai na kansu.
- Su kawo ma’anar muhimman kalmomin da aka yi amfani da su a cikin labarin.
📚 Labari: Karambana Ko Ka Ga Dokin Sarki
Karambana Ko Ka Ga Dokin Sarki
Karambana ya kalli É—an ‘uwansa ya ce, “Ka ga yadda ake yin sitaci”. Shi kuwa Karambana sai ya ce, “Ni kuwa É—an uwa abin da ke bani mamaki ga karan rake, yadda ake samar da sikari daga cikinsa irin wanda muka É—ebo gidan maigari, an ce Turawa ne suka fansar masa da sukari”.
Sai Karambana ya ce, “Babu wani abin mamaki daga cikinsa, bari ka gani”. Sai ya kama hannun É—an ‘uwansa suka sanya cikin jakar Æ™udiri suka runtse idanuwansu. Bayan wani É—an lokaci suka buÉ—e, suna buÉ—e idanuwansu sai Allah ya yassare masu ilimin yadda ake yin rake.
Karambana ya ɗebo karan rake, sannan ya kudurci abin daka. Sai ga turmi da taɓarya da baho da kyalle da tukunya sun faɗo daga cikin jakar. Karambana ya ɓaɓalla karan raken sannan ya zuba cikin turmi, ya shiga bugun karan har sai da ya yi laushi sosai, ya zuba cikin wani baho, ya tace ruwan raken, ya zuba cikin tukunya.
Ya samo Æ™irare, ya kunna wuta, ya É—ora ruwan raken, ya ci gaba da rusa wuta har sai da ruwan raken ya gama siraci sannan ya shanya dallakin sikarin a cikin rana har sai da ya daskare. Karambana ya kalli É—an uwansa ya ce, “Wannan shi ne dallakin sukari”.
Suna cikin wannan wauta sai mai gona ya jiwo ƙaurin wuta, ya zo. Da ya ga irin ɓarnar da suka yi masa, sai ya ɗauko bindiga harba-ruga, amma kafin ya isa inda suke sai suka haɗa hannayensu, suka saka cikin jakar ƙudiri, suka kudurta buƙatarsu watau suna so su koma tsuntsaye. Sannu a hankali suka rikiɗe suka koma Maiki da Mikiya. Suka yi sama fir! Suka bar mai gona yana mamakin irin hatsabibancin waɗannan yara da suka yi masa ɓarna.
Suka yi ta shawagi a cikin dajin Kamuku da ke ƙasar Zazzau wanda ya nausa ya haɗe da dajin Falgore na ƙasar Kano ya dangane da dajin Yankari na ƙasar Bauchi. Suna tafiya suna kallon hotunan namun daji danginsu: zaki, kura, damisa, barewa, bacilmi, ragon daji, raƙumin daji, karkanda, macizai, yanyawa, giwar ruwa, ƙudan tsirya, tsutsar katafila, tsutsar siliki da kwaron luna.
Maiki ya ce da Mikiya, “Shin kin fahimci cewa, dabbobin sun kasu kashi biyu?” Mikiya ta ce, “Eh, na lura wasu dabbobin na rayuwa cikin daji wasu kuma na rayuwa cikin ruwa, wasu jikinsu rufe yake da Æ™wasfa, yayin da wasu jikinsu ke rufe da firkaki wasu kuma gashi ya rufe jikinsu”.
Sai Maiki ya Æ™ara da cewa, “Akwai dabbobi masu Æ™ashin baya É—aya kamar: maciji, kifi, Æ™adangare da kada”. Bayan ya yi shiru sai Mikiya ta ce, “Haka kuma akwai masu tafiya da Æ™afafuwa huÉ—u wasu kuma jan ciki suke yi, yayin da wasu ke tashi sama”.
Maiki ya ce, “Ai in aka lura ma cimakar dabbobin ta bambanta: barewa, giwa, É“eraye, fari, budari duk suna cin tsirrai ne”. Sai Mikiya ta ce, “Amma zaki, kura, damisa, maciji, kare, mangus, jemage, kwaÉ—i da kifi duk suna cin nama ne, waÉ—annan dabbobi ai su ake kira da ‘maciya nama’”.
Mikiya ta É—an yi shiru sannan ta yi fir! Æ™asa. Bayan ta nazarci dabbobin da ke dajin Yankari sai ta koma sama, sannan ta ce, “Hallitar dabbobin ma ta bambanta, Æ™afafuwa da haÆ™oransu an hallice su don su dace da irin abin da suke ci. HaÆ™oran kura dogaye ne masu kaifi za su iya yaga nama”.
Ta haÉ—iyi yawu sannan ta ce, “HaÆ™oran barewa kuwa suna da faÉ—i yadda za su iya tauna tsirrai su niÆ™e su sosai”.
Daga nan Maiki da Mikiya suka ci gaba da shawagi, sun haÉ—u da dabar tsuntsaye da daular zuma da fari. Maiki ya kama sarauniyar fara, fadawanta kuwa suka ce, “Da wa aka haÉ—a mu?” Amma kafin su fara masu da yaÆ™i, sun sauka gefen kogi, suka sake yin siddabaru suka rikiÉ—a suka koma mutane.
Karambana ya yi nitso cikin teku ya kamo sarauniyar kifaye. Suka haÉ—a hallitun don su ga bambancin yadda fara da kifi suke numfashi. Karambana ya É—auko wani katako ya É—ora sarauniyar kifaye sannan ya sanya itace cikin bakinta ya fiddo da muÆ™amuÆ™in kifin, ya yanke su ya bar soson da ke ciki watau ‘gil’ mai ja-ja, ya haska da tabaron hannu da ya É—auko cikin jakar Æ™udiri, ya ce, “Sandunan da ke cikin (watau ‘gil’) mai ja-ja da sosansa masu alamar kaifi su ke motsawa ta hanyar shaÆ™ar iska da fitar da shi, watau shi ne kamar huhun kifi, da shi yake numfashi”.
Karambana ya É—auko sarauniyar fara ya haska cikin bakinta da tabaron hannu sosai ya ga yadda take numfashi, ya ce, “Ita fara ba ta da muÆ™amuÆ™ai kamar kifi (watau ‘gil’), ba ta da huhu, iska na shiga cikin wani kwaroro ne zuwa cikin jikinta”.
Ana kiran wannan kwararo da Karambana ya gani a jikin fara da sunan ‘sifarakul’. Sun yi kama da É—igo-É—igo da ke jikin fara. Daga nan sai suka yi zanen fara da kifi da abubuwan da suka gani a jikin wata takarda sannan suka saka cikin jakar Æ™udiri suka nausa cikin daji suna bin gefen tekun don Æ™ara tantance abubuwan da ke rayuwa a cikin daji.
📖 Bayanin Muhimman Kalmomi
| Kalmomi | Ma’anarsu |
|---|---|
| Karambana | Mutum mai É—aukar magana, wanda duk abun da ya gani ba zai bari ba. |
| ÆŠan uwa | Wanda ake da zumunci na jinni da shi. |
| Sitaci | Wani sinadari da ake fitarwa daga nau’in abinci musamman rogo. |
| Karan rake | Itacen rake wanda ake shukawa a fadama. |
| Sikari | Sinadari mai zaƙi wanda ake fitarwa daga rake. |
| Kudurci | Raya wani abu a cikin rai. |
| Turmi | Abu ne da mata ke daka, ana sassaƙa shi da itace. |
| Taɓarya | Abu ne da ake yin daka da shi. |
| Baho | Mazubi ne, inda ake zuba wani abu. |
| Kyalle | Ragaya da ake samarwa daga tufafi. |
| Tukunya | Abun da ake dafa abinci a ciki. |
| Mikiya | Nau’in tsuntsu ne (namijin maiki). |
| Shawagi | Yawo ko tafiya a sararin samaniya. |
| Yankari | Daji ne da ke yankin Bauchi. |
🎓 Aikin Aji
- Karanta labarin da ke sama a bayyane.
- Fitar da kalmomi masu ma’ana a cikin labarin da ku ka karanta.
© Ilimin Hausa | Bello Hamisu Ida
0 Comments