📚 Kalmomi Masu Ma'ana Ɗaya
About this lesson:
This is a Primary 6 Hausa Language lesson on Kalmomi Masu Ma'ana Ɗaya (Synonyms in Hausa). Pupils will learn how two or more words can have the same meaning and be used interchangeably in sentences.
A1.2 Kalmomi Masu Ma'ana Ɗaya
🎯 Manufar Darasi (Lesson Objectives)
Ɗalibai su koyi kalmomi masu ma'ana ɗaya – wato kalmomi biyu ko fiye da haka da suke nufin abu guda, ko aiki guda. Wannan yana taimakawa wajen faɗaɗa harshe da fahimtar abubuwa cikin sauƙi.
📖 Bayani
- Kalmomi masu ma'ana ɗaya su ne kalmomi guda biyu ko fiye da haka da ke nufin abu ɗaya.
- Za a iya amfani da kowanne daga cikinsu a jimla kuma sakon zai ci gaba da zama daidai.
- Misali: Riga da Taguwa – duka suna nufin tufafi na sama da ake sawa a jiki.
Ana amfani da litattafai, hotuna, katuttuka, da jadawali wajen koyar da darasin. A ƙarshe, a shirya tambayoyi domin jarraba fahimtar ɗalibai.
📋 Misalan Kalmomi Masu Ma'ana Ɗaya
| Kalmomi | Masu Ma'ana Ɗaya |
|---|---|
| Hanya | Titi |
| Riga | Taguwa |
| Rafi | Gulbi |
| Kogi | Ƙorama |
| Dakata | Jira |
| Saurara | Ji |
| Mutuwa | Rasuwa |
| Mage | Kyanwa / Kuliya |
| Babba | Ƙato |
| Hula | Tagiya |
| Kofi | Moɗa |
| Ƙofa | Ƙaure |
| Azure | Garka |
| Kewaye | Banɗaki |
| Aji | Ɗakin-karatu |
| Baba | Abba |
| Mama | Umma |
| Iccen bedi | Iccen dalbeji |
| Wayar tafi da gidanka | Salula |
| Babur | Mashin |
| Koko | Ƙullu / Kamu |
| Karin safe | Kumallo / Kalaci |
| Liƙe / Liƙo | Kari |
| Rufi | Shigifa |
| Ƙorama | Tafki |
📝 Ƙarin Misalai da Jumla
- Saurara = Ji – Misali: Saurara da kyau! → Ji da kyau!
- Koko = Ƙullu – Misali: Na dafa koko → Na dafa Ƙullu.
- Mama = Umma – Misali: Mama ta je kasuwa → Umma ta je kasuwa.
- Wayar tafi da gidanka = Salula – Misali: Ina wayar tafi da gidanka? → Ina salula?
- Mage = Kyanwa – Misali: Mage ta kama bera → Kyanwa ta kama bera.
🎓 Aikin Aji (Class Activities)
- Bayyana kalmomi masu ma'ana ɗaya guda biyar tare da jumla guda ɗaya da ke amfani da kowannensu.
- Ka zana hoton abubuwa biyu da suke da sunaye biyu, ka rubuta sunan farko a ƙasa hagu, sannan na biyu a ƙasa dama.
- Ka binciko kalmomi guda uku da suke da ma'ana ɗaya a cikin wani littafi ko waƙa.
Keywords: Hausa Synonyms, Primary 6 Hausa Language, Kalmomi Masu Ma'ana Ɗaya, Hausa Vocabulary, Hausa Grammar, Hausa Education Nigeria
© Ilimin Hausa | Bello Hamisu Ida
0 Comments