🌍 Sassauƙar Jimla – Hausa Language Lesson (Primary 6)
About this post:
This lesson explains Sassauƙar Jimla (Simple Hausa Sentences) for Primary 6 pupils based on the NERDC 2012 Hausa Language Curriculum.
It includes the meaning, types, examples, and class activities.
A1.1 Tsarin Sassauƙar Jimla
🎯 Manufar Darasi (Lesson Objectives)
- Tantance sassan sassauƙar jimla
- San ma’anar jimla a taƙaice
- Bayyana sassauƙar jimla da kawo misalai
- Yi amfani da littattafai, rediyo, da katuttuka wajen koyarwa
- Amsa tambayoyi a ƙarshen darasi
📖 Ma’anar Sassauƙar Jimla
Sassauƙar jimla ita ce jimlar da take ɗauke da sassan jimla biyu kacal – yankin suna da yankin aiki.
Misalan sassauƙar jimla:
- Audu ya sayi littafi
- Indo tana share gida
- Lado ya ɗauki takalmi
🔹 Ire-Iren Sassauƙar Jimla
1️⃣ Sassauƙar Jimla Mai Aikatau
Ita ce jimlar da take ɗauke da kalmar aiki (aikatau).
Misali: Musa ya ɗebo ruwa
A cikin wannan jimla, Musa ne suna, ya aikata aiki watau ya ɗebo ruwa.
2️⃣ Sassauƙar Jimla Marar Aikatau
Ita ce jimlar da babu aikatau a cikin bayaninta.
Misali: Musa mutum ne mai surutu
📚 Bayanin Sassauƙar Jimla
Sassauƙar jimla tana nufin jeren kalmomi masu bayar da cikakkiyar ma’ana. Yana ƙunshe da suna da abin da aka faɗi game da suna.
Misalan tsarin jimla:
- Audu + ya + sayi littafi
- Indo + tana + share gida
- Lado + ya + ɗauki takalmi
📝 Ƙarin Misalai na Sassauƙar Jimla
- Musa mutum ne mai surutu.
- Rago ɗaya ne a turke.
- Indo ta sayi litattafai.
- Bello yana rubutu.
- Aisha ta tafi makaranta.
- Baba yana noma.
- Yara suna wasa.
- Musa yana wasa da mota.
- Wannan farar mota ce.
🎓 Aikin Aji (Class Activity)
- Rubuta sassauƙar jimla guda biyar.
- Tantance nau’in sassauƙar jimlar da ka rubuta.
© Ilimin Hausa | Bello Hamisu Ida
0 Comments