Hukumar Yansanda Ta Jihar Kano ta Kama Mashahurin Dan Daba Mai Suna Mu'azu Barga

 HUKUMAR ’YAN SANDA TA JIHAR KANO

28 GA YULI, 2025

AIKIN “KUKAN KURA”: AN KAMA MASHAHURIN ƊAN FASHI MU’AZU BARGA DA WASU 14, AN KWATO WAYOYI HUƊU


…Yayin da Rundunar ke ci gaba da yaƙi da dukkan nau’o’in aikata laifi…

Rundunar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta samu nasarar cafke mutane goma sha biyar (15) da ake zargi da aikata laifuka masu nasaba da ta’addanci da fashi, a wani samame na musamman da aka gudanar a Sheka, Ja’oji da Kurna a ranar 26 ga Yuli, 2025. Wannan aiki na daga cikin shirin tsaro na musamman da ake kira “Operation Kukan Kura” wanda kwamishinan ‘yan sanda ya ƙaddamar domin dakile ayyukan laifi tun kafin su faru.

Shirin dai yana kan layi da umarnin Babban Sufetan ‘Yan Sanda na Ƙasa, IGP Kayode Adeolu Egbetokun, PhD, NPM, wanda ke ƙarfafa tsarin tsaron al’umma da haɗin kai da jama’a.

Masu laifin da aka kama, waɗanda shekarunsu ke tsakanin 14 zuwa 28, an same su da wayoyi huɗu (4) da suka kwace daga hannun mutane daban-daban. Sun amsa laifin aikata fashi da sace-sace, musamman satar wayoyi da cin zarafin jama’a.

Cikin waɗanda aka kama akwai shahararren ɗan fashi mai suna Mu’azu Barga, wanda ake zargin ya jagoranci hare-hare daban-daban tare da faɗace-faɗace tsakanin kungiyoyin ‘yan daba a cikin birnin Kano. Za a gurfanar da su a gaban kotu da zarar an kammala bincike.

Kwamishinan ‘Yan Sanda na Jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, PhD, ya bayyana cikakken yaƙi da duk wani nau’i na ta’addanci da dabar ƙungiyoyi, tare da tabbatar da cewa Rundunar za ta ci gaba da tabbatar da zaman lafiya da tsaro a fadin jihar.

Rundunar ta yaba da gudunmuwar al’umma, kuma tana roƙon jama’a da su ci gaba da ba da bayanai masu amfani ta hanyar kai rahoto zuwa ofishin ‘yan sanda mafi kusa ko kiran waɗannan lambobin:

📞 08032419754, 08123821575, 09029292926.

Sanya hannu,

SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ANIPR, MNISMA

Jami’in Hulɗa da Jama’a na ‘Yan Sanda,

Don: Kwamishinan ‘Yan Sanda, Jihar Kano.

Post a Comment

0 Comments