Ƴansanda na bincike kan zargin magidanci da kashe matarsa a jihar Bauchi

Abuja, Najeriya _ Ƴansanda na bincike kan zargin magidanci da kashe matarsa a jihar Bauchi

Ƴansanda

Asalin hoton,NIGERIA POLICE

Rundunar ƴansandan jihar Bauchi da ke arewa maso gabashin Najeriya ta ƙaddamar da bincike kan zargin wani magidanci da kashe matarsa saboda saɓanin da ya shiga tsakaninsu kan abincin buɗa-baki.

A wata sanarwa da kakakin rundunar, CSP Ahmed Mohammed Wakil ya fitar, ya ce lamarin ya auku ne a yankin Fadamar Mada da ke cikin garin Bauchi.

Ya ce, "saɓani ne ya kaure tsakanin wani mai suna Nuru Isah mai shekara 50 da matarsa ta biyu mai suna Wasila Abdullahi kan tsarin abinci da kayan buɗa-baki na gidan."

Ƴansanda sun ce bincike farko na nuna cewa mijin ya yi amfani da bulala wajen bugun matar, "inda ta yanke jiki ta faɗi, da aka kai ta asibitin koyarwa na jami'ar Tafawa Ɓalewa ne likitoci suka tabbatar da rasuwarta."

Sanarwar ta ƙara da cewa ƴansanda sun kama mijin, sun ɗauko bulalar da aka yi amfani da ita, sannan kuma za a yi binciken ƙwaƙwaf a kan gawar.

Post a Comment

0 Comments