Za mu farauto Bello Turji - Inji Sojin Najeriya

 Za mu farauto Bello Turji - Inji Sojin Najeriya

Daga: Bello Hamisu

Earn Some Cash Online

ABUJA, NAJERIYA _ Babban hafsan sojin ƙasar Najeriya, mai suna Laftanar janar Olufemi Oluyede, ya ce sojojinsa za su yi farautar wannan shahararren ɗan bindiga mai suna Bello Turji da hukumomin ƙasar ke nema ruwa a jallo, kuma tun sanda aka fara nemansa yake wasa ɓoyo daga wannan daji zuwa wancan.

Earn Some Cash Online

Babban hafsan ya faɗi haka ne a babban birnin Gusau da ke jihar Zamfara a Arewa maso yammacin ƙasar a lokacin da yake ganawa da manema labarai a hedikwatar shirin sojojin Najeriya da aka yi wa laƙabi da Fansar Yamma, inda ya ce nan ba da daɗewa ba, Turji zai zama labari.

Ya ƙara da cewa,

"Yanzu haka da muke magana da ku, Bello Turji na ta guje-guje, amma duk inda ya ɓuya, za a bi shi, mu yi farautarsa"

Ya ƙara da cewa,

"Ya ci gaba da guje-gujensa, amma zai gama, kuma za mu kama shi,".

Oluyede ya kuma bayyana wasu nasarorin da sojojin suka samu, inda ya ƙara da cewa dakarun ƙasar sun kashe manyan jagororin ƴan bindigar a cikin watannin da suka gabata.

Earn Some Cash Online

Sunan Bello Turji dai ba wani ɓoyayyen suna bane tsakanin ɓarayi  daji, kuma yana daga cikin jagororin ƴan fashin daji waɗanda suka addabi ƙauyukan arewa maso yammacin Najeriya, musamman a jihar Zamfara, wadda rikicin ƴan bindiga ya yi ƙamari.

Earn Some Cash Online

A baya-bayan nan dakarun Najeriya sun matsa ƙaimi wajen kai wa ƴan fashin daji farmaki, a wani yunƙuri na kawar da matsalar tsaro a arewa maso yammacin ƙasar.

Earn Some Cash Online

Sai dai duk da haka ƙauyuka da dama a jihar ta Zamfara, da wasu jihohin masu maƙwaftaka, kamar Sokoto da Katsina na ci gaba da fuskantar hare-haren na ƴan fashin daji.

Earn Some Cash Online

Garuruwan Katsina da Zamfara da Sokoto da Kaduna na ɗaya daga cimin jahohi  dake fama da rashin tsaro a daɗin ƙasar wanda ya sa ƴan ƙasar yin barci da ido ɗaya.

Earn Some Cash Online

Post a Comment

0 Comments