Wata Mata Ta Koma Gida, Ta Samu Gawarwakin Yaranta Mata A Cikin Firji
Daga: Bello Hamisu Ida
ABUJA, NAJERIYA _ Yadda na dawo gida na tarar da gawar ƴaƴana uku a cikin firji'
Ta fara da cewa,
"Na bar yara na uku a gida na je coci, da na dawo gida, gawarsu na tarar".
Wani irin hargitsatsen labari mai ban tausayi da Madam Chikazor Ogachukwu Ejezie ta bayar, matar da ta rasa 'ya'yanta uku a rana ɗaya a yankin Nnewi da ke Anambra.
Ta ci gaba sa cewa, ta bar yaranta uku a gida, ta je jarabawa a yankin Ihiala da ke jihar, amma a lokacin da ta dawo, ba ta tarar da kowa ba a gidan, sannan ƙofar gidanta a buɗe.
Ɗanta namiji da ke cikinsu bai wuce shekara uku ba, su kuma sauran yaranta mata akwai mai shekara bakwai sai kuma shekara tara.
Ta ci gaba da cewa, bayan ta dawo gida sai ta saki jiki tana hira, a tunaninta yaranta sun fita wasa kuma za su dawo, amma har yamma shiru babu alamarsu, a nan ne tsoro ya kamata ta.
Ta ce, "Na tambayi matar abokin mijina da 'ya'yanta suke zuwa coci tare da 'ya'yana, amma sai ta shaida mani cewa a wannan ranar 'ya'yanta ba su fita ba. Sai na tambaye ta ko yarana na gidanta, amma sai ta amsa da cewa ba sa gidan,".
Ta kara da cewa "ɗaya daga cikin makwaftanta sun shaida mata cewa sun ga wasu matasa biyu sun fito daga gidan a wannan rana, kuma sun ga ɗaya daga cikin yarana mata sun fito sun je shago sun yi siyayya, sannan suka koma gida"
Wannan labari ya yi matuƙar tada mata da hankali. Daga nan ne kuma suka fara bincike da neman yaranta duk inda suka san suna zuwa. Daga baya dai suka tsinci gawawwakin yara a cikin firizar gidansu.
Har yanzu an kasa fahimtar yadda waɗannan yara suka shiga cikin firiza kuma an kasa kane cewa ko wani ne ya sa su a firiza, saboda babu wanda ya bada shaidar ganin wani ya shiga gidan.
'Yansandar jihar Anambra sun tabbatar da labarin, sannan sun ce suna bincike.
Irin waɗannan korafe-korafe na mutuwar yara na ƙaruwa a baya-bayanan.
Ko a makonnin baya an rinƙa samun rahotanni na mutuwar wasu yara 'yan gida ɗaya a cikin wata mota da aka ajiye a yankin Nise da ke Anambra.
0 Comments