Matatar man Dangote ta rage farashin man fetur zuwa ₦899
ABUJA, NIJERIYA _ Matatar mai ta ɗangote wadda ta fara tace mai watanni kaɗan da suka gaba ta, ta sanar da rage farashin litar man fetir zuwa naira 899.50 gab da za a yi bukukuwan kirsimati da sabuwar shekara.
Mai magana da yawun matatar wato Anthony Chiejina, ya ce,
"An rage farashin litar man ne domin rage tsadar sufuri ga jama'a, a lokacin shagulgulan ƙarshen shekara".
A cikin watan Nuwambar da ta gabata ne, matatar man mai zaman kanta ta rage farashin litar mai zuwa naira 970.
Ya kuma ƙara da cewa,
“Domin samar da sauƙi kan sufuri a lokacin hutun ƙarshen shekara, matatar mai ta Ɗangote ta fara sayar da mai a kan ragin farashi. Daga yau za a riƙa sayar da man a kan naira 899.50 a kowacce lita, daga mtatar man tamu.''
Chiejina ya ce, matatar Ɗangote ta jajirce wajen tabbatar da ganin an samarwa jama'ar Nijeriya man fetir mai inganci kuma cikin farashi marar tsada.
Wannan, da ma wasu labarai, ku ci gaba da bin shafinmu don samun ingantatattun labaran Nijeriya da kewaye.

0 Comments