An Kama Matar da ke kaiwa Bello Turji Bindigogi

 An Kama Matar da ke kaiwa Bello Turji Bindigogi 

ABUJA, NAJERIYA _ An kama wata mata da ake zargin cewa ita ce ke kaiwa Bello Turji Bindigogi da makamai a Zamfara, jihar da ɓarayin daji suka addaba a ƴan shekarun nan.

Bataliyar rundunar sojin Najeriya mai yaƙi da yan fashin daji a arewa maso yammacin Najeriya da aka sani da sunan Operation Fansar Yamma, ta ci nasarar cafke matar wadda aka ƙiyasta shekarunta 25 da haihuwa tana ɗauke da alburusai 764 da kuma bindigogi har guda shida, waɗanda aka yi zargin cewa za ta kai su zuwa sansanin jagoran ƴan fashin dajin nan Bello Turji, wannan ɓarawon dai ya shahara sosai a faɗin jahar da makwabtanta tun daga Sokoto, Zamfara, Kebbi da Katsina.

Cikin wata sanarwa da kakakin rundunar laftanal kanal Abubakar Abdullahi ya fitar, ya ce,

 "An kama matar ne a ranar 28 ga watan Disamban 2024 da ake ciki, tare da wani mutum da suka yi tafiya tare a yankin Badarawa da ke ƙaramar hukumar Shinkafi ta jihar Zamfara".

An samu nasarar kama su ne bayan wani rahoton sirri da aka samu game da safarar makaman ƴan bindigar a kan hanyar Kware zuwa Badarawa a karamar hukumar ta Shinkafi.

Bayan samun waɗannan bayanai ne dakarun rundunar ta Operation Fansar Yamma suka kafa wani shingen bincike wanda ya kai ga cafke waɗanda ake zargin.

 Ana ci gaba da bincikar mutanen da aka kama.

Sanarwar kamensu ta ƙara da cewa rundunar ta ƙuduri aniyar ci gaba da ɗauka matakan da suka dace domin daƙile safarar makamai ga ƴan bindigar, da ke ci gaba da tayar da zaune tsaye a yankin.

Hukumar ta yi kira ga jama'a da kada su gaji wajen bayar da sahihan bayanan da za su kai ga samun irin wannan nasara, da kama ƴan bindigar da aka jima ana nema ruwa a jallo.

Ire-iren yaran Bello Turji da shi kansa sun  sha sace mata da yara a jihar Zamfara da sauran jahohin dake fama da matsalar tsaro.

Dama dai an jima ana zargin akwai masu kai wa ƴan bindigar makaman da suke amfani da su har dazukan da suke a wannan yanki musamman ita Zamfara, da ta fi fama da wannan matsala.

Ko a watan Nuwamban da ya gabata ma sai da rundunar ƴan Sandar Jihar ta kama wani ɗan ƙasar Aljeriya, mai shekaru 58 kan zargin safarar makamai daga wasu ƙasashe maƙwabtan Najeriya inda ya ke shiga da su ta Zamfara.

Jahohin Katsina da Kaduna da Zamfara da Sokoto sa Kebbi dai na fama da matsalar tsaro wanda ya yi sanadiyar salwantar rayukan ɗaruruwan mutane ya kuma rama wasu da gidajensu.

Daga Arewa360.ng


CODE 1: You

Post a Comment

0 Comments